Bayan koyar da sana’o’in, kazalika an damkawa matan jari don komawa gida su ci gaba da sana’a da hakan zai taimaka mu su wajen kula da yara sakamakon mutuwar mazajen su.
Hauwa Inuwa ita ce ta koyawa zawarawan sana’a da ta hada da da kayan tande-tande da lashe-lashe da kuma tsumi irin na zamani wanda a kan samar daga tsamiya.
Rukaiya Hussaini jami’a ce ta kungiya mai zaman kan ta da ta dukufa ga tallafawa marar sa galihu, ta nuna lamarin taimakawa zawarawa ba ya kadan ko yawa.
Shugaban kwamitin marayun Alhaji Sa’idu Musa Yelwa, ya ce kwamitin zai kara dukufa kan wannan aiki don yadda matan da mazajen su, su ka mutu kan shiga halin kakani-kayi.
An kashe kimanin Naira dubu dari biyar wajen horon da dan jarin da a ka rabawa zawarawan da su ka nufi gida su na murna.
Domin karin bayani saurari rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.
Your browser doesn’t support HTML5