Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Na San Rayuwa Ta Yi Wuya - Goodluck Jonathan


 Goodluck Jonathan, tsohon shugaban Nigeria
Goodluck Jonathan, tsohon shugaban Nigeria

Tsohon shugaban Nigeria cikin gaisuwar tunawa da ranar samun 'yancin Nigeria, ya ce rayuwa ta yi wuya a kasar har ya ce tamkar ta zama hedkwatar talauci a duniya

A wani sakon murnar zagayowar ranar samun 'yancin kai da ya rattabawa hannu, tsohon shugaban Nigeria Dr. Goodluck Jonathan, ya ce ya san rayuwa na da wuya yanzu amma abubuwa za su daidaita nan gaba idan ba'a karaya ba.

Ya ce 'yan Nigeria na da karfin halin jimre duk wata matsala, har ta wuce kuma su fito da karfi. Acewarsa abubuwa sun yi tsamari kuma kasar tamkar ita ce inda talauci ya fi yiwa mutane katutu a duk fadin duniya. Ya ce sanin 'yan Nigeria da karfin halin daurewa za su murmure su fito lafiya bayan da matsalar ta kau.

"Ina mika gaisuwata ga 'yan Nigeria a takaice sai in ce 'Abubuwa za su daidaita'"

"Allah ya albarkaci tarayyar Nigeria da al'ummarta", inji Goodluck Jonathan.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG