An Bada Umarnin Kame 'Yan Kwangilar Ginin Majami'ar Da Ta Ruguje A Uyo

Rugujewar Majami'a A Birnin Oyu

Gwamnan Jihar Akwa Ibom da ke kudancin Nijeriya, inda rufin wata Majami'a ya fadi akan masu ibada a ranar Asabar da ta gabata, in da mutane da yawa suka mutu, ya bada umarnin kama wadanda suka yi kwangilar ginin, cewar wata kafar yada labarai ta jihar.

Gwamna Emmanuel wanda yake a majami'ar yayin da al’amarin ya faru, kuma ya tsira ba tare da jin ko da ciwo, ba ya bada umarnin kamen.

Rahotannin adadin wadanda suka mutu dai sun sha banban tsakanin kafafen yada labaran, inda wasu ke cewa kusan mutane 160 ne suka mutu wasu kuma na cewa sun kusa mutane 60 sannan Jami’an gwamnati na yankin sun ce mutane 27 ne suka mutu yayin da talatin suka ji rauni.

Daruruwan mutane na cikin majami'ar mai suna Reigners Bible Church a birnin na Uyo, a yayin da rufin ya fada musu a ka. Wanda ya kafa majami'ar kuma ya tsira yayin da ala’amarin ya faru za a nada shi ya zama Bishop ne yayin da ake gudanar da ibadar.