Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Hukumar UNHCR Ya Fara Ziyarar Wasu Kasashen Afirka


UNHCR Hukumar dake kula da 'yan gudun hijira
UNHCR Hukumar dake kula da 'yan gudun hijira

Shugaban hukumar UNHCR mai kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, Filipo Grandi, ya fara wata ziyarar kwanaki goma a Najeriya da Nijar da Kamaru da kuma Chadi, domin ganewa idanunsa zahirin halin da ake ciki a sansanonin ‘yan gudun hijirar dake kasashen.

Kwamishina Filipo Grandi, ya fara wannan ziyara ne a yau Litinin da yankin Diffa inda ‘yan Najeriya fiye da 200,000 da suka gudo daga yankin Arewa maso Gabasin kasar suka sami mafaka kusan shekaru uku kanan sakamakon rikicin Boko Haram.

A lokacin da yake tattaunawa da hukumomin Nijar Filipo, yace zai yi amfanin da wannan damar don ganewa idanunsa zahirin halin da ake ciki a sansanonin ‘yan gudun hijira ko da kuwa na wuni daya ne, domin yin hakan yana da muhimmanci sosai.

Wannan rangadin dai yazo ne a dai dai lokacin da kasar Nijar ke tunanin ta inda zata fullowa mawuyacin halin da ‘yan gudun hijirar Najeriya da Mali kimanin dubu dari biyu da sittin da takwas ke ciki, a yayin da kungiyoyin jin kai ke fuskantar rashin kudi a cewar Fara Minista Brigi Rafini.

Domin kwantar da hankulan kasashen da suka karbi wadannan ‘yan gudun hijira Filipo Grandi, ya bayyana cewa a karshen wannan rangadi na kwanaki goma zai kasance wani cikakken lauyan da ya lakanci ainashin bukatun mutanen da yake karewa. Kuma ya baiwa hukumomin Nijar tabbacin ci gaban ayyukan hukumar UNHCR a kasar.

Bayan kasar Nijar shugaban hukumar UNHCR zai ziyarci sansanonin ‘yan gudun hijirar dake Chadi da Kamaru da Najeriya.

Domin karin bayani saurari rahotan Sule Mumuni Barma.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:49 0:00

XS
SM
MD
LG