An Ambaci Wani Sojan Amurka Da Hannu A Kokarin Juyin Mulkin Turkiyya

Wani babban hafsan sojin Amurka yayi Allah wadai da wani rahoto da wata jarida kasar Turkiyya ta buga tana zargin cewa wani tsohon kwamandan Amurka shine ya shirya juyin mulkin da bai yi nasara ba a kasar, ya kira rahoton "maras tushe."

Wata jarida mai ra'ayin rikau da ake kira Yeni Safak ta ambaci wata majiya da ba'a bayyana sunanta ba, da take kusa da magoya bayan juyin mulkin da ake tsare da su, cewa wani tsohon janar na Amurka wanda yayi ritaya bana, wand a ya jagoranci sojojin NATO, yayi ziyarci kasar a asirce sau da dama inda ya raba kudade masu yawa ga wadanda suka shirya juyin mulkin.


Babban hafsan mayaka Amurka Janar Joe Dunford yace abun bakin ciki ne a danganta Janar John Campbell da wannan batu, inji Dunford yayinda yake magana da manema labarai a ma'aikatar tsaron Amurka jiya Litinin.


A halin da ake ciki kuma, Turkiyya ta na auna 'yan Jarida, malaman makarantu, ma'aikatan kamfanin jiragen sama na fasinjar kasar a ci gaba da matakan murkushe wadanda ake zargi suna da dangantaka da wani malamin addinin Islama wanda yake gudun hijira na kashin kai, wanda gwamnatin kasar take zargi a zaman wanda ya kitsa juyin mulkin da bai sami nasara ba.


Gwamnatin kasar a Ankara ta bada sommacin a kama 'yan jarida 42, haka nan an kama malamai 31,haka nan kuma ta kori mutane 211 wadanda suke aiki da kamfanin jiragen sama na fasinjar kasar.