An Ajiye Gawar Jimmy Carter Domin Yin Ban Kwana Da Ita A Birnin Washington

Carter, wanda ya mutu a ranar 29 ga watan Disamban da ya gabata yana da shekaru 100, ya shafe wa'adi daya ne a kan mulki daga 1977 zuwa 1981 sannan ya sha yabo a kan ayyukan jin kan daya runguma bayan shan kaye a zaben shugaban kasa, abin da ya janyo aka bashi lambar girmamawar Nobel a 2002.

A Talatar da ta gabata ne aka yi safarar gawar tsohon Shugaban Amurka Jimmy Carter zuwa ginin Majalisar Dokokin kasar a wani kasaitaccen bikin soja, inda za a ci gaba da ajiyeta domin jama'a suyi bankwana da ita har lokacin da za a yi mata jana'izar kasa nan gaba a makon da muke ciki.

Carter, wanda ya mutu a ranar 29 ga watan Disamban da ya gabata yana da shekaru 100, ya shafe wa'adi daya ne a kan mulki daga 1977 zuwa 1981 sannan ya sha yabo a kan ayyukan jin kan daya runguma bayan shan kaye a zaben shugaban kasa, abin da ya janyo aka bashi lambar girmamawar Nobel a kan zaman lafiya a 2002.

Gawar tasa ta isa ginin Majalisar Dokokin Amurka dake lullube da dusar kankara har zuwa gobe Alhamis, bayan shafe yini guda ana gudanar da shagulgulan bikin safararta daga jiharsa ta asali, Georgia.

Miliyoyin Amurkawa, ciki har da mutanen mahaifar tsohon shugaban kasa Jimmy Carter ta Plains da ke Georgia, za su shafe kwanaki 6 suna ban kwana da tsohon dattijon kasar da ya mutu a makon da ya gabata yana da shekaru 100.