Amurkawa Na Tuna Ranar Harin 11 Ga Watan Satumba

A yau talata Amurkawa suke bakin cikin zagayowar ranar harin ta’addancin 11 ga satumba wanda ya kashe akalla mutane dubu 3 a jihohin New York, da Virginia da kuma Pennyslvania a nan Amurka.

Shugaban Amurka Donald Trump, ya halacir bikin zagayowar ranar 11 ga satumba a Shanksville a jahar Pennyslvania kusa da inda jirgin saman kamfanin united mai lambar tafiya casa’in da uku ya fadi bayan da fasinjojin cikin jirgi suka kwace jirgin daga yan kungiyar ta’addancin al-qaeda da suka yi fashin jirgin.


A ayyanawar shugaban kasar na shekara shekara, ya ayyana 11 ga satumba a zaman ranar kishin kasa, Trump yace wannan mummunar aika aika bata dakushe kudurin kasar akan yanci ba.


Shi kuma, mataimakin shugaban kasa Mike Pence yana halartar bikin a ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ga iyalan wadanda aka kashe lokacin da jirgin saman da aka yi fashin sa ya afkawa ginin.


A can birnin New York kuma, daruruwan mutanen da suka tsira da iyalan wadanda suka mutu zasu ko kuma sun taru a inda tagwayen ginin cibiyar hada hadar kasuwancin kasa da kasa take kafin jiragen saman guda biyu da aka yi fashin, su suka afkawa ginin.