Amurkawa Na Bukin Ranar Shugaban Kasa

(Da ga sama, hagu zuwa dama) Abraham Lincoln, George Washington, Barack Obama, Donald Trump, Franklin Roosevelt, Ronald Reagan, Bill Clinton and Harry Truman.

Duk Litinin ta uku a watan Fabrairu, Amurkawa na gudanar da bukin ranar Shugaban Kasa.

Ranar na kasancewa ne tsakanin ranaikun haihuwar Shugabannin Amurka biyu mafi tasiri kuma wadanda aka fi kauna - Abraham Lincoln da aka haifa a ranar 12 ga watan Febrairu da George Washington da ranar haihuwarsa ta kasance 22 ga watan na Fabrairu.

Kowanne daga cikinsu, na da matukar tasiri wajen kafuwa da bunkasar kasar Amurka.

George Washington ya yi kokari wajen tsara yadda makomar shugabancin Amurka zata kasance, inda ya gabatar da tsare-tsaren da wadanda za su gajeshi za su bi.

Wani muhimmin abinda ya aiwatar a matsayinsa na Shugaban Amurka shine na sauka da ga kan mulki bayan kammala wa’adi biyu na shekaru hudu kowanne, inda ya tabbatar da mika mulki cikin lumana ga magajinsa.

A nasa bangaren, Abraham Lincoln ya rike ragamar shugabancin kasar a dai dai lokacin da take fuskantar barazananr wargajewa sakamakon yakin basasa.

Amurka ta tafka sa’a, bai kasance shugaba ga bangaren da suke samun galaba a yakin ba.

Daf da kawo karshen basasar, sai ya fara tsare-tsaren raba madafun iko tsakanin gwamnatin tarayya da na jihohi.

Sakamakon hakan da yayi, amurka ta kara karfi bayan kammala yakin: inda ta kasance tarayyar gaskiya karkashin kakkarfar gwamnatin tarayya.

A yau, bikin ranar Shugaban Kasa ya karrama duk mutumin da ya taba zama Shugaban Amurka.

Sai dai babu daya daga cikinsu daya samu tasiri, ko ya cancanci irin wannan karramawa kamar, Washington da Lincoln, wadanda suka hada kan kasar akan akidun da har izuwa yau ke tafiyar da kasar da al’ummarta.