An watsa wasan ne cikin harsunan turancin Ingilishi da yaren sifaniya wadanda suka ba da wannan adadi.
Washington D.C. —
Wasan karshe da aka buga tsakanin Faransa da Argentina a gasar cin kofin duniya da aka yi a Qatar, shi ne wasan kwallo na biyu da Amurkawa suka fi kallo.
A ranar Lahadi Argentina ta doke Faransa da ci 4-2 a bugun fenariti.
Bisa alkaluma da kamfanin Nielson da ya kware wajen kididdigar masu kallo da kuma gidan talabijin na Fox da Telemundo, Amurkawa miliyan 25, 783, 000 ne suka kalli wasan na ranar Lahadi.
An watsa wasan ne cikin harsunan turancin Ingilishi da yaren sifaniya wadanda suka ba da wannan adadi.
Wasan kwallo da Amurkawa suka fi kallo shi ne wasan karshe na gasar cin kofin mata ta duniya tsakanin Amurka da Japan a shekarar 2015, wanda ya samu adadin ‘yan kallo miliyan 26.7
Amurka ta doke Japan da ci 5-2.