WASHINGTON, D.C —
Amurka ta soma sauya tsarin sojojinta a Nahiyar Afirka, da ta bada sanarwar za ta dawo da wani bangare na mayakan sojojinta kana ta musanyasu da wasu kwararrun sojojinta masu bada horo.
Jami’an ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon sun bayyana wannan yunkuri a matsayin irinsa na farko, da zai yi tasiri a ayyukan dakarun Amurka da suke aiki a Nahiyar, yayin da take kara maida hankali a kan yaki da ta’addanci da karfin gaske.
A wata sanarwa jiya Laraba, mai magana da yawun ma’aikatar tsaron ta Amurka, Alyssa Farah, ta ce yunkurin zai taimakawa Amurka ta yi gogayya da kasashen China da Rasha a Nahiyar Afirka.
Farah ta ce Amurka za ta soma dawo da dakarun runduna ta 101 ta mayakan sama a cikin ‘yan makwannin nan masu zuwa.