Majalisar dattawan Amurka ta jefa kuri’a jiya Laraba, akan yin dokar kawo karshen yakin da Amurka ke yi a Yemen, wanda kasar Saudiyya ke jagoranta, ‘yan majalisu 63 ne suka goyi bayan matakin, 37 kuma basu amince ba.
Kuri’ar da aka jefa yawanci wata alama ce ga gwamnatin kasar, saboda shugabannin jam’iyyar Republican ba su nuna alamun sun yi na’am da matakin ba.
Wannan kuri’ar da suka jefa wata hujja ce dake nuna barakar dake tsakanin fadar White House da ‘yan majalisar dokokin Amurka game da kasar Saudiyya, duk da cewa manyan jami’an shugaba Donald Trump, a fannin tsaron kasa su biyu, sun gabatar da muhimman bayanai gaban majalisar dattawan.
Kusan watanni biyu bayan da aka kashe wani dan jaridar kasar Saudiya, mai caccakar Yariman masarautar kasar a karamin ofishin Jakadancin Saudiyya dake Santanbul.
Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo, da sakataren tsaron kasar Jim Mattis, sun yi kira da a kula da dadaddar dangantakar kud-da-kud dake tsakanin Saudiyya da Amurka. Ciki, harda gudunmuwar da Amurka ke badawa a yakin da Saudiyyar ke jagoranta a Yemen.
A wani lamari na daban, wasu hare hare ta sama da dakarun Saudiyya ke jagoranta suka kai akan mayakan Houthi, sun hada da makaman da aka siyo daga Amurka. Hare-haren sun yi sanadiyar mutuwar dubban fararen hular Yemen, sun kuma lalata asibitoci tareda ratattaka wasu unguwanni.