Umarnin da zai fara aiki da karfe 11 da minti 59 na daren Litinin saura dakika a shiga ranar Talata, zai bukaci matafiya su saka takunkumin rufe huska a cikin jirgin sama da jirgin ruwa da na kasa da motocin bos da taxi da kowane iri motocin jama’a, za a kuma bukaci a saka takunkumin a wuraren daukar ababen hawa kamar tashoshin mota da filayen jiragen sama da tashoshin jiragen kasa da na ruwa.
A ranar 21 ga watan Janairu, shugaba Joe Biden ya umarci hukumomin gwamnati su gaggauta daukar matakan saka takunkumi a filayen saukar jiragen sama da kuma cikin jiragen kasuwa da cikin jirgin kasa da jiragen ruwa na jama’a da kananan jiragen ruwa da bos bos da duk sufurin jama’a.
A karkashin shugaba Donald Trump wanda ya kammala mulki a ranar 20 ga watan Janairu, hukumar yaki da cuta mai yadon ta nemi bada umarnin tilasta saka takunkumi a cikin sufuri amma hakan bai yiwuwa ba, a maimakon haka sai hukumar ta bada shawarwari masu karfi a kan saka takunkumin.
Kungiyar kamfanonin jiragen sama ta Amurka ta fadawa Biden a cikin wannan wata cewa nan gaba zata hana dubban fasinjoji bulaguro da suka ki biyewa umarnin saka takunkumin.