Amurka na shirin tura wani jirgin ruwa mai dauke da filin tashin jiragen yaki da kuma sojoji zuwa gabas ta tsakiya, a wani mataki da mai ba da shawara kan harkar tsaro na Amurka, John Bolton ya ce, martani ne kan “wasu matakai na barazana da kuma gargadi” kan take-taken Iran.
A cikin wata sanarwa da ya fitar da daren jiya Lahadi, Bolton ya ce, wannan matakin da suka dauka “sako ne na gargadi da ke nuna cewa, duk wani hari da Iran ta kai kan wani abu da Amurka ke da ra’ayi akai, ko wasu kawayenta, zai iya fuskantar zazzafan fushinta.”
Ya kuma kara da cewa, ba wai Amurka “tana neman fada da gwamnatin Iran ba ne, amma a shirye ta ke ta mayar da martani kan wani abu da Iran ke muradinsa, ko akan dakarun juyin-juya halinta ko kuma asalin dakarun kasar.
Sai dai gwamantin Trump ba ta yi cikakken bayani kan takamaiman barazanar da Iran din ta yi ba.
Ya zuwa yanzu, hukumomin Iran su ma ba su ce uffan ba kan wannan sanarwa ta Bolton.