Amurka Za Ta Taimaka Wa Kananan Manoman Afirka

  • Ibrahim Garba

Samar da isasshen abinci kamar haka ka iya rage talauci a Afirka

Amurka ta amince ta taimaka ma kananan manoman Afirka ta yadda gonakinsu za su dada yabanya saboda a rage fatara a nahiyar Afirka.

Amurka ta amince ta taimaka ma kananan manoman Afirka ta yadda gonakinsu za su dada yabanya saboda a rage fatara a nahiyar Afirka.

Sakataren Aikin Gonan Amurka Tom Vilsack ya rattaba hannun kan wata yarjajjeniyar hadin gwiwa a jiya Alhamis da Kungiyar bunkasa noma a Afirka mai suna Alliance for Green Revolution in Africa (AGRA).

Bisa wannan yarjajjeniyar, Amurka da wannan kungiyar ta AGRA za su yi aiki tare don samar da iri da dabarun ni’imta gonaki, da sauran hanyoyin taimakawa manoma su inganta yabanya. Za su kuma rinka horar da manoma kan hanyoyin tafi da sana’ar noma da kuma mafifitan hanyayoyin sayar da amfanin gonaki.

Da farko wannan shirin zai maid a hankali ne kan yadda za a dada bunkasa noman irin amfanin gona a inda aka fai nomansu a yanzu, irinsu Ghana, Kenya, Mali, Tanzania da Mozambique.

Mata ne dai rukunin day a fi yawa a jerin nau’ukan kananan manoma a Afirka. Kungiyar AGRA ta ce inganta fannin noma a Afirka it ace hanya mafi sauke ta rage talauci da kara tasirin mata a cikin al’ummar da su ka fito.