Ma'aikatar tsaron Amurka da ake kira Pentagon, tana duba janye kusan dukkan dakarun Amurka na musamman daga jamhuriyar Nijar, tare da rufe kusan illahirin cibiyoyin yaki da ta'addanci da take dasu a fadin nahiyar Afirka, kamar yadda rahotanni a kafofin yada labarai suka nuna.
WASHINGTON D.C. —
Jami'an Pentagon sun gayawa jaridar New York Times cewa, tashoshin mayakan Amurka dake kamaru, da Kenya, da Libya da Tunisia duk za'a rufe su da zarar sakataren harkokin tsaro Jim Mattis, ya amince da shirin. Amma Amurka zata ci gaba da barin sojoji masu yawa a Najeriya da Somalia.
Kamar yadda jaridar ta New York Times ta fada, matakin canji ne da Amurka ta tsara daga yakar 'yan ta'adda zuwa maida hankali kan manyan yake-yake.
Matakin yana zuwa ne bayan wani harin da mayakan sakai suka kai kan sojojin Amurka a Nijar bara,wadda ya halaka sojojin Amurka hudu, la'marin da ma'aikatar tsaron ta dauki laifin aukuwar sa.