Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Zaben Congo Ta Hana Bemba Tsayawa Takara


Madugun adawa Jean-Pierre Bemba wanda hukumar zaben Congo ta haramtawa shiga takarar shugaban kasa
Madugun adawa Jean-Pierre Bemba wanda hukumar zaben Congo ta haramtawa shiga takarar shugaban kasa

Duk da cewa kotun kasa da kasa kan manyan laifuka ta wanke Jean-Peara Bemba daga zargin da ta yi masa, hukumar zaben Dimokradiyar Congo ta hanashi tsayawa takarar shugabancin kasar da za'a yi 23 ga watan Disambar wannan shekara

Babbar jamiyyar adawa ta kasar Congo mai suna Movement of the Liberation of the Congo(MLC) a takaice wacce ke karkashin Jean-Peara Bemba, tana fafitikar ganin dan takarar ta ya ci gaba da kasancewa cikin jerin ‘yan takara a zaben da za a gudanar a ranar 23 ga watan Disambar wannan shekarar.

Hukumar zaben kasar ta hana Benba tsayawa takara ne biyo bayan gurfanad dashi da babban kotun kasa-da-kasa dake birnin Hague tayi a shekarar 2016.

Kotun tace Bemba wanda shine tsohon mataimakin shugaban kasar Congo shine keda alhakin aikata laifuffukan yaki da sojojin sa kai dake karkashin kulawar sa a jamhuriyar Africa ta Tsakiya suka aikata.

Sai dai a cikin watan yuni kotun tayi watsi da wannan karar kana ta salami Bemba daga gidan yarin da take tsare dashi.

Wannan dalilin ne ya sa jam’iyyar tasa take cewa batun kama shi da kotun ta duniya ta yi wannan tsohon batu ne, don haka a bar Bemba ya tsaya takara.

Sai dai mai sharhi akan harkokin siyasa na kasar Delphin Kapaya ya ce yadda kotun ta gudanar da wannan shara’ar shine zai nuna irin mataki nagaba da magoya bayan Beman zasu dauka.

Ya ce ana iya fuskantar matsala domin ko yana da goyon baya kwarai da gaske, muddin aka hana shi takara kuma dokar kasa ce tace hakan to ba za a samu matsala ba,amma idan domin siyasa ce aka hana shi, ba shakka magoya bayan sa ba zasu amince da hakan ba. Wannan shine zai zamo ummuubaisan rikicin daka iya barkewa

Sai dai bayan an kwashe watanni ana zama cikin halin kila-wa-wakala, Shugaba Joseph Kabila ya amince cewa ba zai tsaya takara ba, bayan ya kwashe shekaru 17 yana mulkin kasar.

Kabila dai shine ya kada Bemba a zaben shekarar 2006, kuma yanzu ya amince ne ya marawa Emanuel Ramazani Shadary baya wanda yake na hannun damar sa ne.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG