Amurka Za Ta Kori Wasu Daliban Kasashen Waje Da Ke Karatu a Kasar

Immigration Deportations

Hukumar da ke kula da dokokin shige da fice ta Amurka wacce ake kira ICE a takaice, ta ce dole ne duk daliban kasashen wajen da ke zaune Amurka, wadanda da za su dauki darrusansu ta yanar gizo a zangon karatu na farkon a lokacin hunturu, su koma kasashensu.

Sai dai har yanzu ba a bayyana adadin daliban da wannan mataki zai shafa ba, amma daliban kasashen waje su ne kan gaba wajen samar da kudaden shiga ga jami’o’i da dama a Amurka saboda suna biyan kudaden karatunsu baki daya.

Hukumar ICE ta ce ba za ta bar daliban da suke rike da viza ta karatu su zauna a kasar ba idan karatunsu gaba daya zai ta’allaka ne kan koyarwa ta yanar gizo.

Ta kara da cewa dole ne daliban su fice daga kasar ko kuma su nemi a yi musu sauyin makaranta kamar yadda sanarwar da hukumar ta fitar ta nuna.

Sai dai matakin bai shafi daliban da ke daukan karatu a aji ba.

Akalla vizar F-1 dubu 388,839 da kuma M-1 dubu 9,518, a ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta bayar kamar yadda alkalumanta suka nuna.