Amurka Za Ta Kara Tallafi Da Ta Ke Badawa A Najeriya

Jekadan Amurka a Najeriya Mr. Richard M. Mills Jr.

Kasar Amurka ta jaddada aniyar ci gaba da bayar da tallafi a Najeriya da kuma inganta shirin yadda zai kara kyautata rayukan 'yan kasar.

Jekadan Amurka a Najeriya Mr. Richard M. Mills ne ya bayyana haka a wata ziyara da ya kai jihar Sokoro. Ya kuma bayyana cewa, yana tattaunawa da mahukunta da jama'a a sassa daban daban domin jin yadda za'a kara inganta shirye-shiryen.

Mr. Richard Mills yace a zaman 'yan watannin da yayi a Najeriya, ya samu dama ta haduwa da al'ummomi su tattauna a kan abubuwa daban daban a dukan sassan kasar.

Yace a kan haka ne ya je Sakkwato a kan muhimmancin da ke gare ta a Najeriya, inda ya tattauna da jama'a da 'yan kasuwa, da shugabanin addini, da dalibai da ma kafafen yada labarai domin ya ji daga bakin su, abinda kasar Amurka ke aiwatarwa a Najeriya da kuma jin shawarwarinsu kan yadda suke ganin za'a kara inganta ayyukan a yankunansu.

Jekadan dai ya yabawa kokarin da hukumomi a Najeriya ke yi wajen ganin sun magance wasu matsaloli da suka addabi jama'a a fannin tsaro, ilimi da bunkasa kiwon lafiya da makamantansu.

Jekadan Amurka a Najeriya Mr. Richard M. Mills Jr.

A jawabinsa, gwaman jihar Sakkwato Ahmad Aliyu Sokoto, ya tabbatar da cewa, lallai jama'a sun amfana gaya daga ayyukan da kasar Amurka ta gudanar kuma ta ke kan gudanarwa a cikin jihar.

Yace ayyukan sun hada da taimakawa ga kyautata rayukan jama'a a fannin kiwon lafiya, tallafawa jama'a wajen saukaka halin kuncin rayuwa, rage fatara da horas da jama'a a kan kyakkyawan tsarin dimokradiya da sauransu, da yace suna yabawa da kuma suna neman kari.

A nashi bayanin, shugaban hadakar kungiyoyin fafatuka Bello Shehu Gwadabawa, wadanda ke sa ido ko aiwatar da wadansu ayyukan hadaka da kasar Amurka ke gudanarwa, yace ba don tallafin da USAID ke bayarwa a sassa daban daban ba, da moriyar da a ka samu a sassan ba a same ta ba.

Najeriya duk da kasancewar ta daya daga cikin kasashe mafiya girma da karfin tattalin arzika a nahiyar Afirka, akwai wasu kalubalayye da ke yi mata tarnaki wajen samar da dukan ci gaba da ake bukata ga jama'arta, abinda ya sa kasashen da suka ci gaba ke bayar da tallafi a kasar ta fuskoki mabambanta.

Bayanai sun nuna kasar Amurka ta hannun hukumar raya kasashe, ta soma baiwa Najeriya tallafi a fannin ilimi tun a shekara ta 1960, lokacin da kasar ta samu 'yancin kai.

Wannan ya ci gaba inda ya fadada zuwa sassa da suka hada da bunkasa ayyukan noma. Kiwon lafiya, tattalin arziki, karfafa dimokradiya, kawar da fatara, kyautata shugabanci, da sauran sassan ci gaba, a jihohi daban daban.

Saurari cikakken rahoton Muhammad Nasir daga Sakkwato:

Your browser doesn’t support HTML5

Amurka Za Ta Kara Tallafi Da Ta Ke Badawa A Najeriya