A yayin da ya ke gabatar da lambar karramawar ga hukumar raya kasashe ta Amurka, USAID, shugaban majalisar sarakunan Fulanin Ghana, Sarki Muhammad Idris Bingil ya ce hakika ayukan hukumar ta USAID sun yi tasiri kwarai da gaske ga rayuwar al'ummar Fulani a fadin kasar.
Hukumar ta USAID ta koyar da sarakunan Fulani fiye da dari daya akan sha'anin jagoranci na gari, warware rikice-rikice da haɗin kai tsakanin al'umma.
Masana harkar tsaro sun ce wannan zai ba da gudummawa sosai wajen shawo kan matsalar rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma da ke ci gaba da yin barazana ga tsaron kasa.
Wakilin hukumar USAID a taron karramawar Olivier Gerrard ya bayyana farin ciki kan wannan karramawar, da kuma ganin cewa ayukan hukumar sun yi tasiri kan al'ummomi, ta yadda za su kuma karfafa samar da ci gaba mai dorewa.
Gerrard ya ce hukumar za ta kuma ba da himma wajen ganin al'ummar sun yi aiki da ilimin da aka koyar da su domin ci gaban kasar ta Ghana.
Akan haka yayi kira ga hukumomin kasar da su dora daga inda hukumar ta tsaya, ta hanyar kara fadakarwa da janyo jama'a a jiki, ta yadda za su fahimci muhimmancin zaman lafiya wajen samar da ko wane irin ci gaba, musamman a tsakanin manoma da makiyaya.
Kasar ta Ghana na daga cikin kasashen da ke fama da rikici tsakanin manoma da makiyaya, wanda a lokuta da dama kan yi sanadiyyar rasa rayuka da dukiyoyi.
Saurari sautin cikakken rahoton Hamid Mahmoud:
Dandalin Mu Tattauna