Amurka ta sanar da wani tsarin takaita biza ga mutanen da hukumomin Washington ke ganin suna da alhakin haifar da cikas ga tsarin dimokradiyya a Ghana, gabanin zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokokin kasar da za a gudanar a watan Disamba a kasar wacce ke Yammacin Afirka.
"Wannan tsarin takaita biza zai shafi wasu mutanen da ke cin dunduniyar tsarin dimokradiyya ne kawai kuma ba ana nufin za ta shafi al’ummar Ghana ba ko kuma gwamnatin Ghana," in ji Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken a wata sanarwa da ofishinsa ya fitar a ranar Litinin.
Sanarwar na zuwa ne a daidai lokacin da Ghana ke shirin gudanar da zaben shugaban kasa a watan Disambar 2024.
Amurka kan yi amfani da tsarin takaita biza a matsayin hanya ta hukunta wasu manyan mutane da za su iya kasancewa masu zaman kansu ko jami’an gwamnati a kasashe da dama.
A cewar sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen ta fitar, Amurka ta kuduri aniyyar tallafawa da inganta dimokradiyya a Ghana da ma duk duniya baki daya.