Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben Ghana: Sojin Kasar Sun Yi Damarar Samar Da Zaman Lafiya


Babban hafsan sojin kasar Ghana, Manjo Janar Bismarck Kwasi Onwona
Babban hafsan sojin kasar Ghana, Manjo Janar Bismarck Kwasi Onwona

Babban hafsan sojin kasar Ghana, Manjo Janar Bismarck Kwasi Onwona, ya gargadi sojojin kasar Ghana da su kaucewa yaudarar ‘yan siyasa kana kar su karkata ta wani bangare siyasa gabanin babban zabe na watan Disamban shekarar 2024.

Ya kuma jaddada bukatar jami’an soji su nuna kwarewa ba tare da shiga harkokin siyasa ba a daidai lokacin da kasar ke tinkarar wannan lokacin mai muhimmanci.

Da yake jawabi a kan rawar da sojojin ke takawa wajen wanzar da zaman lafiya a lokacin zaben, Manjo Janar Onwona ya jaddada aniyar rundunar sojin ta ci gaba da tabbatar da kwarewa.

Ya yi kira ga daukacin jami’an soja da su mai da hankali kan ayyukansu domin tabbatar da cewa an gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali da lumana, yana mai tabbatar wa ‘yan kasar Ghana a shirye sojojin suke wajen kare kasar a lokacin zabe.

A jawabinsa, Manjo Janar Onwona ya kuma yi kira ga kafafen yada labarai da su yi aiki yadda ya kamata, inda ya bukace su da su guji yada labaran karya da na kirkira.

Ya kuma yi gargadin cewa bada rahotanni marasa tushe na iya yin barazana ga zaman lafiyar kasar da tada fitina, musamman a lokacin zabe mai matukar muhimmanci.

“Ban ware wani rukuni na mutane ba. Abin da nake nufi shi ne, kada wani ya yaudaresu; kama daga ‘yan siyasa, ‘yan jarida, ko kuma ‘yan kasuwa”.

“Mu ba ‘yan siyasa ba ne, aikinmu shi ne kare Kundin Tsarin Mulki. Don haka, ina magana ne ga kowa da kowa da ke da niyyar yaudarar kowane jami’in Sojojin ta hanyar da bai dace ba, ”in ji shi.

Shugaban rundunar sojin ya yi wannan jawabi ne a lokacin kaddamar da wani sabon wurin kwana ga jami’an da ke babban ofishin rundunar da ke Kumasi.

An gudanar da aikin ne da nufin inganta rayuwar jami'an soji, wanda ke karkashin kulawar Birgediya Janar Michael Kwadwo Opoku, babban kwamandan runduna ta tsakiya.

Ana sa ran sabon ginin da aka kaddamar zai inganta jin dadin jami’an soji da ke yankin, a daidai lokacin da rundunar ke shirin tallafawa kokarin kasar na gudanar da zabe cikin nasara da lumana a cikin watan Disamba.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG