Amurka ta ce kamata ya yi kungiyar kasashen Afirka, ta fito fili, kiri-kiri, ta gayawa shugaba Cote d’Ivoire Laurent Gbagbo cewa dole ya mika mulki.
Da ya ke magana a jiya alhamis a birnin Nairobin kasar Kenya, mataimakin sakatariyar harakokin wajen Amurka, James Steinberg ya fada cewa Amurka ta yi amanna,abokin jayayyar Mr.Gbagbo, Alassane Ouattara , shi ne ya yi nasara a zaben da aka yi kwanan nan a kasar, kuma shi ya kamata ya yi shugabancin kasar.
Ya bayyana fatan cewa kwamitin shugabannin kasashen Afirkan da aka dorawa nauyin warware rikicin siyasar kasar Cote d’Ivoire zai iya shank an Mr.Gbagbo ya yi murabus.
Mr.Gbagbo ya tsaya kai da fata cewa shi ne ya yi nasara a zaben. Ya bijirewa kakkarfar matsin lambar da kasashen duniya su kai mi shi don su tilasta mi shi mika mulki.
A ranar 28 ga watan jiya na janairu, kungiyar kasashen Afirka ta cimma jituwar kafa kwamitin warware rikicin kasar na Cote d’Ivoire. Amma a farkon wannan mako ofishin Mr.Gbagbo ya yi sanarwar cewa, shugaban zai yi watsi da duk wani sakamakon binciken da zai nuna cewa ya sha kaye a zaben.