Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Tana Goyon Ba A Kafa Takunkumin Cinikin Coa-Coa Kan Ivory Coast.


Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton da takwaran aikinta na Mexico
Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton da takwaran aikinta na Mexico

Amurka ta bayyana goyon bayanta ga kiranda Alassane Ouattara mutuminda Duniya duka ta amince shine ya lashe zaben Ivory, na hana sayen Coa-Coa daga kasar na tsawon wata daya.

Amurka ta bayyana goyon bayanta ga kiranda Alassane Ouattara mutuminda Duniya duka ta amince shine ya lashe zaben Ivory,na hana sayen Coa-Coa daga kasar na tsawon wata daya.

kakakin Ma’aiatar harkokin wajen Amurka,PJ.Crowley,yace wan nan hanye ce ta tilastawa Laurent Gbagbo,ya mika mulki ga Mr.Ouattara.

Jiya litinin ce wani kamfani Amurka mai cibiya a Minnesota, Cargill,da ya shahara wajen sayen Coa-Coa daga Cote D’Voire,ya bada sanarwar dakatarda sayen amfanin gonan daga kasar. Hanin na wata daya an dauke shi ne da nufin hana Mr. Gbagbo kudade.

Babu tabbas ko sauran masu sayen cocoa cocoa,suma zasu dauki wan nan mataki.Sabodahaka ne ma farashinsa ya tashi da kamar kashi 4 a hadahadarsa a Ingila jiya litinin.

XS
SM
MD
LG