Fadar White House ta nan Amurka, jiya Laraba tayi ALLAH waddarai da Karin kudin fiton da kasar Turkiyya tayi wa Amurka akan kayayyakin Amurka da ake shiga dasu cikin kasar.
Wannan dai shine fito na fiton da kasashen biyu kawayen juna dake cikin kungiyar tsaro ta NATO suke yi a tsakanin su.
Yanzu haka dai Turkiyyarta kara kudin haraji akan kayayyakin Amurka da suka hada da Motocin shiga,Giya,da gawayi da dai sauran wasu abubuwa, Karin wanda yakai na dala miliyan 533 kenan.
Turkiyyar tayi hakan ko a matsayin martini na karin kudin da Shugaba Trump yayi na ninka kudin tama da karafa da kasar ke kaiwa Amurka.
Wannan matakin na Amurka ko ya samo asali ne na kin da kasar ta Turkiyya tayi na sakin wani Ba’Amurke Pasto mai suna Andrew Brunson da take tsare dashi akan zargin leken asiri da kuma wasu ayyukan dake da nasaba da taadanci.
Mai Magana da yawun Fadar ta White House Serah Hukabee Sanders tace wannan Karin kudin fiton da kasar Turkiyya tayi abintakaici ne domin ko ta bar jaki ne ta kama bugun taiki.