Amurka Ta Yi Allah Wadai Da Hare Haren Da Aka Kai Kabul

Da kakkausan harshe Amurka ta yi Allah wadai da munanan hare-hare na baya-bayan nan da aka kai birnin Kabul, da su ka kashe tare da raunata dinbin jami'an tsaro da farar hula, yayin da ta ke kuma baiwa Afghanistan tabbacin cewa za ta hada kai da ita don tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali da kuma cigaban kasar.

Tuni kungiyar Taliban ta dau alhakin kai wadannan hare-haren.

Mai magana da yawun Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka Mark Toner ya fadi jiya Talata cewa Amurka za ta cigaba da tattaunawa da Afganistan da Pakistan don kakkabe harkokin ta'addanci a kasashen biyu.

Tagwayen hare-haren kunar bakin waken da aka kai wuri mai cike da hada-hada a Kabul, su ne na farko a jerin hare-haren na ranar Litini, sannan sai wani harin da aka kai da mota 'yan sa'oi bayan nan a wani wurin da ke daura da ofisoshin gwamnati da na diflomasiyya. Daga nan kuma wasu 'yan bindiga su uku su ka ja daga daura da wani ginin gwamnati wanda ke kusa da ginin wata kungiyar agaji, wadda ake kira Care Internationa, wanda aka yi kaca-kaca da shi.

Wani jami'in gwamnatin Afghanistan ya ce jami'an tsaro sun hallaka dukkan 'yan bindiga ukun wanda ya kawo karshen mamayar ta tsawon sa'o'i a cikin dare.

Tun da dadewa gwamnatin Afghanistan ke zargin kasar Pakistan, musamman ma cibiyoyin sojinta, da goyon bayan 'yan tawayen Taliban cikin sirri a Afghanistan.