Kwamitin mai mambobin kasashe 15, ya yanke shawara kan wannan matsayar jiya Talata, 'yan sa'o'i kawai da kammala taron gaggawa. Da gagarumin rinjaye Kwamitin ya yanke shawara cewa kaddamar da makamai masu linzami uku samfurin Rodong da Koriya Ta Arewa ta yi ranar Litini, wadadan su ka shafe kilomita 1,000 kafin su ka fado, bayan shigarsu yankin tsaron sararin saman Japan, wata babbar sabawa ce ga nauyin da ya rataya a wuyar Janhuriyar Jama'ar Koriya a matakin kasa da kasa bisa ga jerin tanaje-tanajen Kudurin Kwamitin Sulhun MDD.
Gaggauta yanke shawarar da Kwamitin ya yi, alamace cewa China na dada fusata da take-taken makiran aminanta. Kaddamar da makamai masu linzami a wannan satin na zuwa ne a daidai lokacin da China ke karbar bakuncin babban taron Shugabannin kasashen duniya na G-20.
Mambobin Kwamitin sun gargadi Koriya Ta Arewa da ta tsai da komai, ciki har da gwaje-gwajen nukiliya, wanda hakan ya saba ma tanaje-tanajen kudurorin Kwamitin Sulhun, ta kuma mutunta duk kudurorin. Kwamitin Sulhun ya kuma umurci sashin da ke kula da batutuwan takunkumi da ya himmantu ga aiwatar da su, ya kuma kira kasashen duniya da su kara azama wajen aiwatar da matakan da aka dauka bisa tanaje-tanajen Kwamitin Sulhun.