Mai’aikatar harkokin wajen Amurka ta kawo karshen taimakon shekara da shekaru da take yiwa Falasdinu a jiya Juma’a, tana mai cewar gwamnatin tayi nazari sosai kuma ta fahimci Amurka ba zata iya ci gaba da bada wannan taimakon ga hukumar aiki da raba kayan taimako ta MDD.
Mai Magana da yawun hukumar aiki da raba kayan taimako ta MDD Chris Gunness, yace da kakkausar murya hukumarsa ta yi watsi da wannan zargi cewa ta gaza a wurin shirye shiryenta na makarantu da cibiyoyin kiwon lafiya da shirin raba kayan taimako.
Yace babban bankin duniya ya kwatanta aikin hukumar a matsayin babban alheri ga duniya, kuma bankin ya yaba mana a kan gudanar da tsarin makaranta mai inganci a yankin, wanda a koda yaushe daliban mu suna fice a kan takwarorinsu na makarantun gwamnati.
A makon da ya gabata ne gwamnatin Trump tace zata yanke dala miliyon 200 daga taimako da tattalin arzikin kasar ke bayarwa ga Falasdinawa, biyo bayan nazari da tayi a kan ayyukan taimako a yammacin kogin Jordan da kuma zirin Gaza.