Sakataren tsaron Amurka, Jim Mattis, ya ce ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon, ba za ta janye atisayen da sojojinta za su yi nan gaba da Korea ta Kudu ba.
“Mun dauki matakin janye da yawa daga cikin manyan atisayen sojin ne da kyakkyawar manufa, bayan taron kolin da aka yi a Singapore” Inji Mattis, wanda ke nuni da taron kolin da aka yi a ranar 12 ga watan Yuni, tsakanin shugaba Donald Trump da takwaran aikinsa na Korea ta Arewa, Kim Jong Un.
Tun bayan wannan taro ne kuma, dangantaka tsakanin hukumomin Washington da na Pyongyang ta tabarbare.
A ranar Juma’a, Trump ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa ya umurci Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo da ya soke wata ziyarar da ya shirya kai wa Korea ta Arewa saboda, a cewar Trump “ba a samun ci gaban da ya kamata, kan batun kwance damarar makamin nukiliya a yankin tekun Korean.”
Hukumomin na Pyongyang, sun cika alkawarinsu na maido da abin da ya saura daga gawarwakin sojojin Amurka da aka kashe a lokacin yakin Korea, sannan sun jingine duk wani shirin gwaje-gwajen makamai masu linzami, amma kuma babu wata alama da ke nuna cewa sun himmatu wajen wargaza makaman na nukiliyan kasar.
Da aka tambayi Mattis ko suna duba yiwuwar komawa gudanar da atisayen sojin da suke yi, sai ya kaucewa wannan tambayar.
Facebook Forum