Kasar Amurka ta tallafawa Jamhuriyar Nijar da kayayyakin soja da nufin karfafawa dakarun kasar gwiwa na yakin da su ke yi da kungiyoyin ‘yan ta’adda a yankin Sahel.
Jakadan Amurka a Nijar Amb. Eric P. Whitaker, ya mikawa hukumomin tsaron Jamhuriyar Nijar makullan wata babbar cibiyar samar da bayanai da bada umarnin soja.
Gwamnatin Amurka ta gina cibiyar tare da saka na’urori sadarwa na zamani, wanda kudinsu ya kai Dalar Amurka miliyan 16.5 kwatankwacin CFA miliyan 8000.
Jamhuriyar Nijar na ci gaba da daukan matakan murkushe kungiyoyin ‘yan ta’adda da suka addabi jama’ar kasashen Sahel.
Da yake karbar tallafin Ministan harkokin cikin Gidan Nijar Bazoum Mohamed ya ce, sun ji dadi sosai da wannan cibiya kuma za su yi amfani da na’urorin da ke cikin ta domin ci gaba da yaki da ta’addanci.
Saurari cikakken rahoton Sule Mumuni Barma daga Yamai:
Your browser doesn’t support HTML5