Amurka Ta Tallafawa Nijar Da Motocin Soja Domin Yaki Da Ta'addanci

Gwamnatin Amurka ta baiwa Jamhuriyar Nijar tallafin motoci ga sojojin kasar, wadanda kudinsu suka haura dala milliyan daya, da nufin karfafawa kasar ta Nijar guiwa a yakin da take yi da ‘yan ta’adda.

Amurka Ta Bawa Nijar Tallafin Motocin Soji

A yayin wani bikin musamman da aka gudanar a cibiyar ajiyar kayayakin sojoji dake birnin Yamai, jakadan Amurka a Nijar din Eric P. Whitaker ya hannuntawa hukumomin tsaron Nijar tallafin, da ya hada da motocin soja da tantunan tanpol na ajiyar kayan soja, a matsayin wani bangare na gudunmawar da Amurka ke bayarwa domin ayyukan samarda tsaro a yankin Sahel.

Jami’in hulda da ‘yan jarida a ofishin jakadancin Amurka a Nijar Elhadji Idi Baraou ya yi Karin bayani, inda ya ce, tallafin yana da mutukar muhimmanci a yakin da kasar Nijar take yi da ta’addanci.

Amurka Ta Bawa Nijar Tallafin Motocin Soji

Da yake karbar makullan motoci Ministan tsaron Nijar Pr. Issouhou Katambe ya yaba da gudunmawar ta gwamnatin Amurka, domin abu ne da zai taimakawa sojojin Nijar a yaki da kungiyoyin ta’addanci.

Saurari Karin bayani cikin sauti Souley Moumouni Barma.

Your browser doesn’t support HTML5

Amurka Ta Bawa Nijar Tallafin Motocin Soja Domin Yaki da Ta'addanci