A Jamhuriyar Nijar jam’iyar hamayya ta MPN Kishin Kasa ta bayyana damuwa game da makomar karatun yara sakamakon abin da ta kira rikon sakainar kashin da gwamnatin kasar ke yi wa sha’anin ilimi ganin yadda hukumomi ke kokarin takaita al’amuran koyarwa a bana duk da irin koma bayan da anobar cutar coronavirus ta haddasawa wannan fanni.
A taron manema labaran da suka kira a karkashin jagorancin shugaban jam’iyar adawa ta MPN Kishin Kasa, Alhaji Ibrahim Yacouba, kusoshin jami’iyar sun bayyana rashin gamsuwa da tsare tsaren da gwamnatin Nijar ta sa gaba wajen sake bude makarantu a ranar 1 ga watan yunin gobe inda suka yi zargin cewa akwai dalilan siyasa wajen daukar wannan mataki.
Wannan ya sa jam’iyar ta MPN Kishin Kasa ke gargadin hukumomin ilimi su tuntubi dukkan masu hannu a sha’anin karatun boko don zakulo hanyoyin warware matsalolin da ke addabar wannan fannin da a can dama ke cikin wani mawuyacin hali inji shuwagabaninta.
Dan majalisar dokokin kasa Korone Masani shi ne mataimakin shugaban wannan jam’iyya ya ce “a cikin sabon tsarin da za a fara, ajin da ke da mutum 50 za su je makaranta da safe da kuma maraice, amma ajin da ke da mutum tamanin kuma za su yi karatu sau daya ne a rana.”
“Daga nan ma kun ga an nuna bambanci ai,” a cewar dan majalisar.
A matsayin martani shugaban ma’aikata a ofishin ministan ilimi a matakin firaimare Ashana Hima ya ce da yawun kungiyoyin malamai da na iyayen yara suke tsare tsaren sake bude makarantu.
A ranar 20 ga watan Maris ne hukumomin Nijar suka rufe illahirin makarantun bokon kasar wato kwana daya bayan da aka gano bullar kwayar cutar corona a kasar.
Amma lura da abin da aka kira nasarorin da aka samu a yunkurin murkushe wannan cuta ya sa gwamnatin kasar yanke shawarar sake bude makarantu a ranar 1 ga watan Yuni.
Facebook Forum