A ci gaba da tallafawa matasan Najeriya duk shekara a fannin ilmi, bana ma ofishin jakadancin Amurka da ke Najeriya ya bai wa wasu 'yan Najeriyar guraben karo ilmi a jami'o'i da kwalejojin ilmi da ke sassa daban na Amurka.
Da yake jawabi yayin bikin ban-kwana da daliban, mataimakin jakadan Amurka a Najeriya, Sir Earton Smith, ya ce a bana kadai kimanin hazikan daliban Najeriya 130 ne suka sami nasarar samun guraben, wanda hakan na cikin wani bangare na shirin bunkasa ilmi da ofishin jakadancin keyi.
Da takewa muryar Amurkac karin bayani, jami''ar sashen ilmi na ofishin jakadancin Amurkan a Najeriya, Miss Malate Ann Atajiri tace suna zakulo zakakkuran matasa ne marasa hali daga sassa daban daban na Najeriys don daukar hidimar karatunsu a Amurkan.
Tace karatun ya kunshi matakin karatu na digiri har zuwa digirin digirgir, da kuma ake sa ran bayan kammala karatun nasu zasu dawo gida su taimaka wajen gina kasa.
A saurari cikakken rahoton wakilin Muryar Amurka
Your browser doesn’t support HTML5