Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka Matthew Miller ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar jiya Litinin cewa, "Amurka ta tabbatar da juyin mulkin soja a Gabon." Miller ya ce an dakatar da taimakon na wani dan lokaci tun ranar 26 ga Satumba. Miller ya ce duk "taimakon jin kai, lafiya, da ilimi" ga Gabon zai ci gaba.
Wani gungun hafsoshin soji karkashin jagorancin Janar Brice Clotaire Oligui Nguema, babban hafsan tsaron fadar shugaban kasa, sun yi wa shugaba Ali Bongo daurin talala a gidan a ranar 30 ga watan Agusta tare da kwace mulki. An nada Janar Nguema a matsayin shugaban kwamitin da a karshe zai mayar da mulki ga gwamnatin farar hula.
Sojojin da suka yi bore sun sanar da juyin mulkin a gidan talabijin na kasar jim kadan bayan da hukumar zaben kasar ta bayyana cewa Bongo ya sake lashe zaben kasar karo na uku a babban zaben kasar da aka gudanar kwanakin kafin juyin mulki.
A shekara ta 2009 ne Bongo ya fara mulki bayan rasuwar mahaifinsa Omar Bongo wanda ya shafe shekaru 42 yana mulkin kasar mai arzikin man fetur.
'Yan adawa sun ce iyalan sun gaza raba arzikin man fetur da na ma'adinan kasar ga al'ummarta miliyan 2.3.
Judd Devermont, mataimaki na musamman ga shugaban Amurka Joe Biden, ya gana da Nguema da Firaministan da sojoji suka nada Raymond Ndong Sima a makon jiya a Libreville babban birnin kasar, inda suka tattauna hanyar da za a bi wajen maido da dimokradiyya a Gabon.
Gidan Talabijin na Gabon ya ruwaito kalaman Nguema bayan taro, inda ya nanata cewa zai mayar da mulki ga farar hula a karshen mulkin sojan, amma bai bayyana lokaci ba.
“Amurka ta kara jaddada aniyar mu ta tallafa wa Gabon wajen komawa ga gudanar da tsarin mulkin farar hula cikin lokaci kuma mai dorewa,” in ji Miller a cikin sanarwarsa. "Za mu dawo da taimakon mu tare da ayyukan da gwamnatin rikon kwarya ta yi na tabbatar da mulkin dimokradiyya."