Ba ‘yan asalin kasar Somaliya kadai ake mayarwa kasarsu ba. A cikin watanni uku na farko, a shekaran nan ta dubu biyu da goma sha bakwai, Amurka ta bada umarnin mayar da ‘yan asalin kasar Afrika dubu daya da dari biyu, bisa ga rahoton wata cibiyar bincike ta jami’ar Syracuse. Kasashen da suka fi yawan mutanen da aka mayar kasashensu sun hada da Ghana, Najeriya, Somalia da kuma Kenya.
Umarnin maida mutanen kasashensu na asali ya sabawa abinda yake faruwa a shekarun baya. Daga shekara ta dubu biyu da shida zuwa dubu biyu da goma sha shidda, adadin ‘yan asalin Afrika da ake tasa keyarsu daga Amurka ya ragu daga dubu biyu da dari daya zuwa dubu daya. Zuwa karshen shekar nan, adadin wadanda za a mayar kasashensu zai ruba har sau hudu, adadin wadanda aka mayar kasashensu bara, idan aka ci gaba da tasa keyar mutane kamar yadda ake yi a halin yanzu.