Kwamandan jandarmomin jamhuriyar Kamaru John Baptist Makam ya dauki matakan kara karfafa tsaro a duk fadin kasar.
Kwamandan ya umurci jandarmomin kasar baki daya da su sake jajircewa wajen ganin an zakulo duk wanda ake kyautata zaton yana da hannu a hare-haren da Boko Haram ke yawan kaiwa musamman ma a jihar arewa mai nisa.
Kwamandan yace zasu yi kokari matuka gaya su kare kasarsu daga ayyukan ta'addanci da 'yan ta'addan Boko Haram. A cewarsa yanzu zasu soma shiga gida gida domin zakulo 'yan ta'addan daga inda suke boyewa tare da kama makamai.
Dangane da abun da zasu yi idan har sun kama makamai a gidajen mutane, kwamandan yace zasu mika mutanen ga kotun soja domin yi masu hukumcin da ya dace.
Malam Yau dan kungiyar kare hakkin bil'Adama ya bayyana tsoronsu dangane da binciken gida gida saboda kowane lokaci gwamnatin Kamaru tayi hakan ta kan take hakkin mutane, injishi. Yace suna rokon gwamnati idan ta yi aikin tayi da tsoron Allah tare da kare hakkin mutum.
Ko a karshen makon da ya gabata sai da 'yan ta'adda suka kai hari a wasu kauyukan garin Kwalkwata.
Ga rahoton Muhammad Awal Garba
Facebook Forum