Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cutar Ebola Ta Sake Bula A Kasar Congo


Ana yi duk abinda ya kamata domin fuskatar wannan anobar domin ya an bukaci jama'ar kasar da kada su tada hankalinsu

Kungiyar Lafiya ta duniya tace jamhuriyar Congo ta sake fuskantar bular anobar mumunar kwayar cutar Ebola.

Jiya Asabar Ministan lafiya na kasar Congo Oly Ilunga ya bada sanarwar cewa kwayar cutar zazzabin Ebola ta kashe mutane uku a arewa maso gabashin kasar.

Mr Ilunga ya fadawa yan kasar kada hankalinsu ya tashi, jami’an kasar sun dauki dukkan matakan da suka kamata na tinkarar bular anobar wannan cutar.

Kungiyar lafiya ta Duniya tace yanzu haka tana aiki da hukumomin Congo domin tura jami’an lafiya zuwa yankin da mutanen suka mutu a ranar ashirin da biyu ga watan Afrilu. Ana tsamanin kuma akwai mutane goma sha daya da suka harbu da kwayar cutar a wannan yankin.

A ranar Juma’a direktan kungiyar lafiya ta duniya mai kula da Afrika Matshidiso Moeti ya kai ziyara Kinshasa babban birnin Congo domin yin shawarwari akan yadda zasu tinkari bular anobar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG