Amurka ta kawo cikas ga wata bukata da aka gabatar a gaban kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, bukatar da ta nuna a binciki zargin amfani da harsashai na gaske da dakarun Isra’ila suka yi amfani da su akan Falasadinawa,
A ranar Juma'ar da ta gabata dakarun Isra'ilan suka far wa wadanda suka fita domin yin zanga zanga a yankin zirin Gaza.
Wani jami’in diflomasiyan Faransa ne da ke kwamitin ya bayyanawa kamfanin dillancin labaran kasar ta Faransa matakin da Amurkan ta dauka na dakile bukatar ta neman a gudanar da binciken.
Hukumomin yankin Falasdinawa sun ce akalla mutane 15 dakarun Isra’ilan suka kashe a ranar Juma’a, sannan sama da 750, sun samu raunuka daga harbin bindiga.
A jiya Asabar aka yi jana’izar wadanda suka mutun, inda mahalarta jana’izar suka rika kiran da a dauki fansa.
Firai ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, ya jinjinawa sojojin kasar da suka harbi Falasdinawan.
A cewarsa matakin, yunkuri ne na kare ‘yancin gashin kan kasar da kuma tabbatar da tsaron al’umar Isra’ilan.