Ayman al-Zawahiri ya gaji Osama bin Laden a matsayin shugaban al-Qaida bayan shekaru da dama a matsayin babban mai shirya ta kuma mai tsara dabarunta, amma rashin kwarjininsa da gogayya daga masu fafutukar kafa daular Islama ya sa ya zabura da kai hare-hare a kasashen yamma.
An kashe Al-Zawahiri mai shekaru 71 a karshen mako a wani harin da jiragen yakin Amurka suka kai masa, kamar yadda jami'an Amurka suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters a ranar Litinin.
Al-Zawahiri ya kalli yadda al-Qaida ta yi watsi da tashe-tashen hankula sakamakon tawayen Larabawa na shekara 2010 zuwa 2011, wanda masu fafutuka da masu matsakaicin ra'ayi da masana masu adawa da mulkin kama-karya na shekaru da dama suka kaddamar.
A cikin shekaru da suka biyo bayan mutuwar bin Laden, hare-haren da Amurka ta kai ta sama sun kashe mataimakan al-Zawahiri, wanda ya raunana karfin tsageran Masar su sami damar hada kansu a duniya.
Ku Duba Wannan Ma Zawahiri Ne Sabon Shugaban Al QaidaDuk da cewa al-Zawahiri ya yi suna a matsayin mutum mai sassaucin ra'ayi kuma mai fada, al-Zawahiri ya yi nasarar raya kungiyoyin da ba su da alaka da su a fadin duniya wadanda suka karu wajen kai munanan tashe-tashen hankula na cikin gida, wasu daga cikinsu sun samo asali ne daga hargitsin da ya taso daga kasashen Larabawa. Tashin hankalin ya hargitsa kasashe da dama a fadin Asiya da Afirka da kuma Gabas ta Tsakiya.
Amma kwanakin a matsayin al-Qaida na jagora, wadanda suka shirya kai wa Amurka hari a ranar 11 ga Satumba na shekarar 2001, sun dade da barin doron kasa. Don haka, tsagerancin ya koma tushensa a tashe-tashen hankula na cikin gida, lamarin da haddasa cudanya da korafe-korafe a cikin gida da kuma tunzura kungiyoyin Jihadi na kasashen duniya masu amfani da kafafen sada zumunta.
Al-Zawahiri ya kwashe shekaru masu yawa a matsayin mai kishin musulunci.
A karon farko da duniya ta ji labarinsa shi ne lokacin da ya tsaya a kejin shari'a bayan ya kashe shugaban Masar Anwar Sadat a shekarar 1981.
Al-Zawahiri dai ya shafe shekaru uku a gidan yari bisa samunsa da laifin mallakar makamai ba bisa ka'ida ba amma aka wanke shi daga manyan laifuffuka.