Amurka Ta Kama Wani Dan Leken Asirin China

Amurka tana tuhumar wani ‘dan leken asirin kasar China da laifin yunkurin satar bayanan sirri na cinikayya daga wasu manyan kamfanonin jiragen sama da na hanyoyin sufurin sama.

Jiya Laraba ne ma’aikatar Shari’a ta Amurka ta sanar da cewa ta kama Yanjun Xu a Belgium ranar 1 ga watan Afrilu, ta kuma dauko shi zuwan nan Amurka ranar Talata.

Ta ce Xu na daya daga cikin manyan mambobin ma’aikatar leken asirin China, wadda mambobinta ke da izinin yin leken asiri a china da fadin duniya.

A cewar tuhumar da ake masa, Xu ya hada kai da wasu kwararru dake aiki a kamfanonin sufurin sama na Amurka, dake aiki a cikin da wajen Amurka, inda zasu ke zuwa china da zummar koyarwa a wasu jami’u. China ce ke daukar nauyin tafiye-tafiyensu tana kuma biyansu.

Ma’aikatar Shari’ar Amurka dai ba ta bayar da cikakken bayani ba kan yadda Xu yayi kokarin kai hannunsa kan bayanan sirri da kuma yadda aka kama shi ba.