Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben Brazil: Za a Je Zagaye Na Biyu Tsakanin Haddad da Jair


Fireworks light up the sky during the closing ceremony of the Beijing 2022 Winter Olympic Games, at the National Stadium, known as the Bird's Nest, in Beijing.
Fireworks light up the sky during the closing ceremony of the Beijing 2022 Winter Olympic Games, at the National Stadium, known as the Bird's Nest, in Beijing.

Kallo ya koma kasar Brazil, inda za a buga a zagaye na biyu tsakanin Haddad, mai ra'ayin sassauci da Jair, wanda ake ma lakabin Donald Trump din Brazil, saboda ra'ayin rikau dinsa.

Bayan an kidaya kuri'u fiye da 99%, a zaben Shugaban kasar Brazil, dan takarar shugaban kasa mai ra'ayin rikau Jair Bolsonaro ya ci zagaye na farko, inda ya samu kashi 46% na kuri'un da aka kada. To sai dai wannan nasarar bazatar da ya yi, ba ta kai yadda za ta iya kau da yin zagaye na biyu na zaben ba, wanda za a yi ranar 28 ga watan nan na Oktoba.

Ba zato ba tsammani Bolsonaro, dan shekaru 63 da haihuwa, ya zarce gaba dab da zaben na ranar Lahadi, kuma saura kadan kawai ya ci kashi 50% na kuri'un, wanda shi ake bukata a ci ba tare da zuwa zagaye na biyu ba.

Shi tsohon Keftin din soji ne mai ra'ayin rikau wanda ya jinjina ma mulkin soji da aka yi a kasar irin na kama karya, ya kuma ci mutunci 'yan luwadi har ma da mata da kuma bakaken fatan kasar. Ya ma taba gaya ma wata 'yar siyasa cewa ba ta ma da kyawun da har zai yi sha'awar yin mata fade, ya kuma ce babu yadda za a yi a kaunaci dansa muddun ya kasance dan luwadi.

Wannan ra'ayi na Bolsonaro ya sa ana masa lakabi da "Donald
Trump na kasar," wato saboda kamanceceniyarsa da Shugaban Amurka mai irin wannan ra'ayin mai cike da takaddama.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG