A jiya Alhamis shugaban Amurka Donald Trump ya tabbatar da mutuwar shugaban al-Qaida a wani harin jirgi mara matuki da Amurka ta kai a Yemen.
Shugaba Trump ya ce Amurka ta kai harin da yayi nasara na yaki da ‘yan ta’adda da ya kashe Qasim al-Rimi, wanda shine ya kafa kungiyar kuma shugaban kungiyar al-Qa’ida a yankin kasashen Larabawa, reshe kuma ga kungiyar ‘yan ta’addan. Shine mataimakin shugaban al-Qa’ida Ayman al-Zawahiri.
Rimi ya shiga kungiyar al-Qa’ida a shekarar 1990, yana yiwa Osama bin Ladan aiki a Afghanistan kana yana da hannu a wasu kulle kulle da yawa da aka auna Amurkawa.
Rimi shine dan ta'adda na uku mai muhimmanci da aka kashe a yaki da ‘yan ta’adda da Amurka ke yi da ta'ddanci a kashe a cikin watannin nan. A cikin watan Oktoba Amurka ta kashe shugaban kungiyar IS Abubakar al-Baghdadi, a watan Janairu Amurka ta kai hari da jirgi mara matuki da ya kashe babban janar din sojan Iran, Qassem Soleimani.