Ofishin wakilan cinakayya na Amurka ya ce an ‘dage zuwa ranar 15 ga watan Satumba.harajin da za a saka wa kayayyaki irinsu kananan komfutoci na laptop da allon komfuta na monitor, da wayoyin hannu da na’urar wasannin wasa kwakwalwa da wasu kayan wasan yara da takalma da kuma kayayyakin sakawa,
‘Dage saka wannan haraji da aka yi zai taimaka wa Amurkawa, wadanda ke sayen irin wadannan kayayyaki domin bayar da kyautarsu lokacin bukin Kirsimeti.
“Abin da muka yi shine, mun jinkirta ne ta yadda ba zai shafi sayayyar bukin Kirsimeti ba, koda zai iya shafar mutane,” abin da Shuguban Amurka Donald Trump ya fada jiya Talata kenan.
Haka kuma, Amurka ta janye haraji baki ‘daya ga wasu masu shigar da kayayyakin China da suka hada da kayayyakin kiwon lafiya da kare lafiya da na tsaron kasa da sauransu