Fadar Shugaban Amurka ta White House ta kira tattaunawar “mai ma’ana” sannan ta kara da cewa, “satar fasaha, da batun kare kayan fasahar mai shi, da hidimomi da na wasu shingaye baya ga haraji, da batun noma” na daga cikin batutuwan da aka tattauna a kai.
“Bangaren China ya tabbatar da alkawarinsa na kara yawan albarkatun gona da China ke sayowa daga Amurka,” a cewar Fadar Shugaban Amurka ta White House. Takardar bayanin ta Fadar White House ta kuma ce Amurka na sa ran za a cigaba da “tattaunawa kan yarjajjeniyar cinakayya irin wacce za a iya aiwatarwa a birnin Washington DC a farkon watan Satumba.”
Rahoton kamfanin dillancin labaran gwamnatin China, Xinhua, ya ce, tattaunawar ta kasance abin da ya kira, “ta tsakani da Allah, mai matukar inganci da kuma ma’ana,” kuma wakilai a wurin tattaunawar sun tabo abin da ya kira, “batun kara yawan albarkatun gona da China za ta rika sayowa daga Amurka.”
Facebook Forum