A karon farko a tarihi, Amurka ta janye daga jefa kuri’a akan kudurin da aka gabatar a MDD na cire takunkumin tattalin arziki da kasuwanci da aka dorawa kasar Cuba tun kamar shekaru 60 da suka wuce.
WASHINGTON, DC —
Tun shekaru 25 da suka wuce, kowace shekarfa sai MDD ta nemi kasashe su jefa kujri’a akan maganarkawo karshen wannan takunkumi da aka kakabawa Cuba a zamanin yakin cacar baki tsakanin kasashen Yammaci da na gabascin Turai.
A waccan shekara dukkan kasashen duniya, in banda Amurka da Isra’ila,sun jefa kujrik’ar amincewa da a cire wannan takunkumin.
Amma kuwa a wannan shaekar kasashen biyu (Amurka da Isra’ila) sun janye daga jefa kowace irin kuri’a.
A duk kowace shekara Amurka takan jefa kuri’ar rashin amincewa da a cire takunkumin, amma, a cewar jakadiyar Amurka a MDD, Samantha Power, a wannan shekara abubuwa sun chanja kuma manufar bata aiki.