Kasar Australia tace za’a yi amfani da jirgin karkashin ruwa mara matuki, wajen neman jirgin saman Malaysia mai lambar tafiya 370 da ya bace shekarun baya.
Hukumar kare Haduran Sufuri ta Autralia ta fadi yau Laraba cewa zata saka jirgin karkashin ruwa mara matukin a daya daga cikin jiragen ruwa masu binciken teku mai zurfi don ya taimaka wajen nazarin baraguzai da dama da aka gano a binciken da ya gabata, ganin da alamar daga abubuwan da dan adam ya kera ne baraguzan su ka fito.
Za’a gudanar da bincken ne daura da gabar yamma ta Australiar, inda jami'an bincike suka ce sun gano tarkace sama da 20 masu alaka da kerarren abu, wadanda ke bukatar karin bincike.
Jirgin saman Malaysia ya bace ne sama da shekaru biyu da suka gabata ranar 8 ga watan Maris na shekarar 2014, yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Beijing daga Kuala Lumpur. Fasinjoji 239 ne suke cikin jirgin.
Duk da neman da akai tayi a gabar ruwan Autraliar da kewaye, inda masu bincike ke kyautata zaton nan ne jirgin ya fadi, ba’a ga alamar jirgin ko mutanen dake ciki ba.