Wata motar 'yansanda ta sheko a guje cikin masu zanga-zangar kyamar manufofin Amurka da su ka yi gangami a harabar Ofishin Jakadancin Amurka dake Manila, babban birnin kasar ta Philippines a yau dinan Laraba. Ta raunata mutane da dama.
Mutane wajen 1,000 ne suka taru a gaban ofishin Jakadancin Amurka din suka bukaci Amurka ta kawo karshen kasancewarta a Philippines. 'Yansanda sun harba barkonon tsohuwa da kuma ruwan zafi don tarwatsa cincirindon mutanen.
Hotunan talabijan sun nuna masu zanga-zanga zagaye da motar 'yansanda suna ta bugunta da katako, kafin direban ya shiga markade masu zanga-zangar akai-akai.
Daya daga cikin jagororin masu zanga-zangar mai suna Renato Reyes, yace saida aka kai akalla uku daga cikin masu zanga-zangar zuwa asibiti, bayan da motar 'yansandan ta kade su.
An kama masu zanga-zangar da dama yayin wannan zanga-zangar, bayan da su ka watsa ma wasu 'yansanda jan fenti.