: Masu gabatar da kara a madadin gwamnatin tarayyar Amurka, sun gabatar da tuhumar aikata ta’addanci ga dan kasar Uzbekistan din nan, wanda ake zargi da amfani da wata motar daukar kaya ya kade mutane takwas a birnin New York.
Mutumin, dan shekaru 29 da haihuwa, ‘yan sanda sun harbe shi a ciki.
Tuhume-tuhumen da ake masa sun hada da na taimaka ma wata kungiyar ta’addanci da kuma lalata motoci. Ba a tantance ko yaushe zai fara gurfana a gaban kotu ba.
An zargi Saipov da shekowa da motar daukar kayan da ya yi hayarta, ya doshi cincirindon jama’a da ke tafiya a lawalin masu keke a Manhattan a ranar Talata, inda ya markade mahaya keke da matafiya da kafa.
Daga bisani motar ta gwabji wata motar bus ta ‘yan makaranta, sai Saipov ya diro daga motar daukar kayan. Ya riko wasu kananan bindigogi biyu kafin wani dan sandan New York ya harbe shi.
Masu bincike, wadanda su ka yi tambayoyi ma Saipov yayin da ya ke kan gadonsa na asibiti, sun ce ya shafe makwanni ya na shirya kai harin.