Ofishin jakadancin Amurka dake Nijar ne ya gayyaci Farfasa Attahiru Jega zuwa kasar domin taimakawa hukumar zaben Nijar din wato CENI ta magance matsalar da take fuskanta.
Farfasa Jega zai karawa CENI dabarun tsara zabe yadda zai zama da inganci da adalci yayinda take shirin tsara zaben shugaban kasa zagaye na biyu.
Farfasa Jega yace sun yi anfani da damar da karawa juna ilimi. Ya bada kasida ga ma'aikatan CENI tare da ziyartar duk manya manyan 'yan siyasa da suke da rawar da zasu taka a zaben. Ya ziyarci hukumar dake kokarin kawo daidaituwa tsakanin 'yan siyasa wato CNDP. Ya sadu da wakilan hadakar jam'iyyun siyasa dake adawa da ake kira COPA. Haka ma ya gana da wakilan kungiyoyin dake goyon bayan jam'iyyar dake mulki yanzu.
Dangane da koke-koken 'yan adawa yace a yi kokari a tattauna domin a samu masalaha a kuma yi tafiya tare. Kowane zabe akan samu kace na ce amma 'yan siyasa suna da haki su tattauna a samu masalaha domin kasa ta cigaba.
Shugabannin hukumar zaben Nijar CENI sun bayyana gamsuwa da gudummawar Farfasa Jega kuma a cewar mataimakiyar shugaban CENI Hajiya Maryama Katambe akwai abu da yawa da suka karu dasu har da litattafai da ya basu.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5