Amurka ta gargadi Rasha kada ta kuskura ta yiwa zaben bana katsalandan

John Bolton, mai baiwa shugaban Amurka shawara akan harkokin tsaro

John Bolton mai ba shugaban Amurka shawara akan harkokin tsaro ya gargadi Rasha kada ta yi kuskuren yiwa zaben wannan shekarar katsalandan yayinda yake tattaunawa da takwaran aikinsa na kasar Rasha din

Mai bai wa shugaban Amurka shawara kan harkokin tsaro na kasa John Bolton, ya gargadi takwaran aikinsa na Rasha, da kada su kuskura su yi katsalandan a zaben tsakiyar wa’adi da za a yi a watan Nuwamba.

Bolton ya fito karara, ya ce Amurka a shirye take ta dauki duk matakan da suka dace, domin hana hakan daga aukuwa.

Bolton ya yi wadannan kalaman ne a Geneve, inda ya hadu da Darektan harkokin tsaron kasa na Rasha, Nikolai Patrushev.

A cewar Bolton, wannan batu na gargadi da ya yi wa Rashan, shi ya hana fitar da wata matsaya ta hadin gwiwa daga bangarorin biyu a karshen taron, wanda shi ne na farko da manyan jami’an kasashen biyu suka yi, tun bayan ganawar Shugaba Trump da takwaran aikinsa na Rasha, Vladimir Putin suka yi a Helsinki a watan da ya gabata.

Hukumomin tattara bayanan sirri a nan Amurka dai sun ce lallai Rasha ta yi katsalandan a zaben kasar a zaben 2016, zargin da Rashan ta sha musantawa.