Amurka Ta Gargadi Mahukunta A Sudan Su Kyale Masu Zanga Zanga

Wasu masu zanga zanga a Sudan

Amurka tayi kira ga jami’an tsaro da sojojin kasar Sudan cewa kada su yi amfani da karfin tuwo a kan wadanda zasu gudanar da gagarumar zanga zanga a gobe Lahadi talatin ga wata Yuni.

Ranar talatin ga watan Yuni, rana Kenan da kungiyar Tarayyar Afrika ta baiwa gwamnatin soji ta wucin gadi a Sudan ta mika mulki ga farar hula. Kasar Sudan ta koma karkashin mulkin sojoji tun bayan hambarar da dadadden shugaban kasar Omar al-Bashir a ranar 11 ga watan Afrilu. Ranar talatin ga wata Yuni, wata ranar ce da kasar ke tuna juyin mulki da al-Bashir ya yi a shekarar 1989.

Wani babban jami’in Amurka ya fadawa manema labarai a ranar Alhamis cewa babban sako mai muhimmaci shine kada a yi tashin hankali, ya kuma kara da cewa mutane Sudan da fararen hula a kasar suna da hurumin shirya taron jama’a.

Babban jami’in na Amurka yace aza takunkumai na cikin matakan da za a iya dauka idan aka kawo tashin hankali a kan fararen hula.

Muna da ‘yancin daukar martani da duk mataki da muka ga ya dace, inji jami’in na Amurka.